9 Mayu 2020 - 05:44
Sudan : Kotu Ta Kwace Kaddarorin Makusantan Al-Bashir

Wata kotu a kasar Sudan, ta kwace kaddarorin wasu makusantan hambararen shugaban kasar Umar Hassan Al-Bashir, kamar yadda kwamnitin musamman da aka kafa domin bibiyar zargin cin hanci da rashawa da ake wa tsohon shugaban kasar ya sanar.

(ABNA24.com) Wata kotu a kasar Sudan, ta kwace kaddarorin wasu makusantan hambararen shugaban kasar Umar Hassan Al-Bashir, kamar yadda kwamnitin musamman da aka kafa domin bibiyar zargin cin hanci da rashawa da ake wa tsohon shugaban kasar ya sanar.

Wani mamba a kwamitin mai suna, Wadji Saleh, ya shaida cewa, girman cin hancin da rashawa da tsohon shugaban kasar ya aikata lokacin yana mulki ta wuce duk wani tunani.

Kaddarorin da aka kwace sun hada da gidaje na katsaita, da filaye masu fadi, wandanda kuma duk na makusantan tsohon shugaban ne, da suka hada da sirikansa, da ‘ya ya ‘yan uwansa da kuma tsofafin ministoci, wandanda suka mallaki dukiyoyin ta hanyar da bata dace ba a cewar kwamitin.

Wannan babban sako ne ga tsaffin magabatan kasar da kuma masu mulki a yanzu inji kwamitin.

Dama kafin hakan dai hambararen shugaban kasar Umar Al-bashir da ya mulki kasar na tsawan shekaru 30, na fuskantar daurin shekaru biyu dama wasu tuhume tuhume, bisa kisan masu zanga zanga.


/129